Merkel ta yi fatali da wasikar da shugaba Ahmedinijad ya aike mata | Labarai | DW | 22.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta yi fatali da wasikar da shugaba Ahmedinijad ya aike mata

SGJ Angela Merkel ta yi watsi da wata wasika da shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nijad ya aika mata inda ya ke bukatar hadin kan Jamus. Merkel ta fadawa wata tashar telebijin ta Jamus cewa wasikar ta nanata matsayin da shugaba Ahmedi Nijad ya dauka a baya wanda ko kadan ba abin karbuwa ba ne ga Jamus. Ta ce wasikar ta saka ayar tambaya game da ´yancin wanzuwar Isra´ila, abin da ke kasancewa wani bangare na manufofin ketare na Jamus. Merkel ta ce takardar ba ta ma yi tsokaci ba game da tayin da Jamus da sauran manyan daulolin yamma suka gabatar ba da nufin warware fito na fiton da ake yi da gwamnatin Iran akan shirin ta na nukiliya.