1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yabawa kudurin mdd akan Iran

December 24, 2006
https://p.dw.com/p/BuWd

Jamus tayi maraba da takunkumin baui daya da wakilan komitin sulhun mdd suka cimmawa jiya akan harkokin nuclearn kasar Iran.Shugabar gwamnati Angela Merkel da ministan harkokin ketare na kasar Fran Walter-Steinmeier,na ganin wannan mataki a matsayin muhimmin gargadi wa Iran,na cikan kaidoji da cikanta alkawarin da aka cimma na kasa da kasa.

Merkel ta bayyana cewa yanayin cimma wannan daidaito tsakanin wakilai ,na nuni da yadda alummomin kasashen duniya suka hada kai na ganin cewa an samo bakin zaren warware wannan rikicin Nuclear ta Iran da murya guda.Jamus dai ta jagoranci wasu manyan kasashe wajen kokarin shawo kann Iran adangane da hrkokin bunkasa sinadranta na uranium.Duk dacewa jamus bata cikin komitin sulhun mdd,ita da wakilan komitin masu zaunannun kujera biyar suka rubuta wannan kuduri da aka amince dashi jiya.