1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta yaba da shirin maido da taimakon kudi ga Falasdinawa

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Masar Hosni Mubarak sun yi maraba da sake mayar da shirin taimakon kudi ga al´umar Falasdinawa. Shugabannin biyu sun bayyana haka a wurin cin abinci rana da aka shiryawa shugaba Mubarak wanda ke wata ziyarar aiki ta yini 3 a nan Jamus. A jiya sassan nan 4 dake shiga tsakani wajen warware rikicin yankin GTT wato Amirka, KTT, Rasha da kuma MDD suka amince da dawo da wannan shiri na wa´adin watanni 3 a matsayin gwaji ko gwamnatin Falasdinawa karkashin jagorancin Hamas zata canza matsayin ta na nuna adawa da wanzuwar Isra´ila.