1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta tattauna da Bush a fadar White House

January 14, 2006
https://p.dw.com/p/BvCP

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yaba da wani sabon babi na huldar dangantaku tsakanin Jamus da Amirka bayan tattaunawar da ta yi da shugaba GWB a fadar White House. Merkel wadda ke ziyarar aiki ta farko a Amirka tun bayan da ta dare kan kujerar shugabar gwamnati, ta ce da akwai damar bude wani yanayi na yarda da juna. Ta ce tattaunawar da suka yi da shugaba Bush sun hada da batutuwan da kasashen biyu suka samu sabani akai kamar sansanin Guantanamo inda Amirka take tsare da firsinonin da take zargi da laifin ta´addanci. Bush ya yi watsi da sukar da Merkel ta yi yana mai cewa gidan yaren na da muhimmanci da tsaron lafiyar Amirka. Shugabannin biyu sun kuma tattauna game da rikicin nukiliyar Iran wanda suka ce sun fi son a warware shi ta hanyar diplomasiya. Dangantaka tsakanin Jamus da Amirka ta yi tsami a ´yan shekaru sakamakon adawar da Jamus ta nunawa yakin da Amirka ta kaddamar akan Iraqi.