Merkel ta soke ziyararta a Aljeriya | Labarai | DW | 20.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta soke ziyararta a Aljeriya

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta dage ziyarar aiki ta yini biyu zuwa kasar Aljeria da ta shirya fara wa a wanna Litinin din 20 ga watan Fabarairun da muke ciki.

Shugabara gwamnatin Jamus Angela Merkel

Shugabara gwamnatin Jamus Angela Merkel

Rahotanni sun nunar da cewa Merkel ta dage wannan ziyarar ne sakamakon rashin lafiyar shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika da aka ce ta yi kamari. Kamfanin dillancin labaran kasar ta Aljeriya APS, ya ruwaito cewa Shugaba Bouteflika na fama da matsalar sarkewar numfashi. Tun da fari dai an shirya cewa shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel za ta ziyarci Aljeriya tare da ganawa da Firaministan kasar a wannan Litinin din 20 ga watan Fabarairun da muke ciki kana a ranar Talata 21 ga watan na fabarairu ta gana da Shugaba Bouteflika.

Dama dai Shugaba Bouteflika ya sha fama da rashin lafiya a shekara ta 2013. Mai kimanin shekaru 79 a duniya da ke zaman tsohon dan gwagwarmaya ne a lokacin neman 'yanci kan kasar kana ya kwashe tsahon shekaru 15 a kan karagar mulki.