1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta nuna takaici kan kalaman Trump

November 23, 2016

Shugabar gwamnatin Jamus ta nuna takaici kan kalaman shugaban Amirka mai jiran gado Donald Trump bisa kasuwanci tsakanin bangarorin.

https://p.dw.com/p/2T75p
Bundestag Generaldebatte  Angela Merkel
Hoto: Getty Images/AFP/T. Schwarz

Shugabwar gwamnatin Jamus Angela Merkel a wannan Laraba ta facaccaki matakin shugaban Amirka mai jiran gado Donald Trump kan shirin ficewa nan take daga yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen da tekun Pacific ya ratsa. Ana tattauna yarjejeniyar karkashin Shugaba Barack Obama na Amirka mai barin gado. Shugabar gwamnatin ta Jamus Merkel ta yi kalaman a gaban majalisar dokokin inda take cewa babu wanda zai amfana da soke yarjejeniyar kasuwancin.

Shugabar gwamnatin ta Jamus ta kuma nuna takaici bisa rikicin Siriya da ake kai hare-hare kan asibitoci da yadda Rasha take ci gaba da goyon bayan Shugaba Bashar al-Assad na kasar ta Siriya. Kana Angela Merkel ta ce gwamnatin Jamus za ta ci gaba da hadin kai da Turkiyya kan fannoni masu muhimmanci tsakanin bangarorin biyu.