1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

D Merkel Regierungserklärung

September 8, 2009

Jawabin shugabar gwamnatin Jamus a gaban Majalisar Tarayya

https://p.dw.com/p/JXvK
Angela MerkelHoto: picture alliance/dpa

A lokacin da ta fara jawabin ta, Angela Merkel tayi magana game da mummunan dauki ba dadi tsakanin sojojin na Jamus da yan Taliban. Tace abin takaici ne a sami koda mutum guda ya rasa ransa a kasar ta Afghanistan, kuma tace a madadin majalisar dokoki ta Bundestag, tana baiyana bakin cikin taa game da mace macen da aka samu lokacin harin. To amma tace bisa manufa, tana goyon bayan aiyukan da sojojin na Jamus suke yi a kasar ta Afghanistan.

Tace aiyukan da sojojin na Jamus suke yi, aiyuka ne da ake matukar bukatar su domin tabbatar da tsaron kasar mu. Wadannan aiyuka an dangana su ne da kudirorin majalisar dinkin duniya. Tura soijojin mu da aka yi, tun shekara ta 2002, mataki ne da ya sami amincewar dukkanin gwmanatocin da suka yi mulki a Jamus tun daga wannan lokaci. Kara wa'adin zaman sojojin da kuma daidai yawan su da bukatun aiyukan su a can, matakai ne dakan sami goyon baya mai yawa a majalisar dokoki. Hakan kuwa yana da matukar muhimanci ga sojojin mu dake can.

Shugabangwamnati Angela Merkel tayi amfani da kalmomi masu karfi domin adawa da masu sukan harin da sojojin na Jamus suka kaiwa tankunan daukar man guda biyu da yan Taliban suka yi fashin su, matakin da ya haddasa samun mace-mace, ba tare da masu sukan sun jira an kammala binciken ainihin abin da ya faru ba.

Irin wannan ra'ayi ne shima ministan harkokin waje, Frank Walter Steinmeier ya nunar a jawabin sa, ko da shike ya nuna fahimta a game da muhawarar da ta taso, game da aiyukan rundunar ta Jamus a Afghanistan. Duk da hakan ya nunar a fili cewar:

Kafin a kammala binciken abin da ya faru, aka shiga sukan Jamus a cikin gida da ketare. Saboda haka ne na tattauna ta wayar tarho tare da ministocin harkokin wajen kasashen Turai tun daga karshen makon jiya, na kuma gaya masu cewar ya kamata su dakata tukuna har sai an kare bincike.

A lokacin da ake muhawara a majaisar dokokin ta Jamus, kungiyar Nato a karon farko ta sanar da cewar farar hula suna daga cikin wadanda suka mutu a lokacin harin na sojojin Jamus. Shima a fakaice, ministan tsaron Jamus, Franz Josef Jung ya amince da hakan.

Idan har a wannan hari an sami farar hula da suka mutu, to kuwa wannan abin dake bukatar ta'aziyyar mu ne. Zamu kuma tabbatar da ganin al'amura sun daidaita a wannan wuri. INa ganin hakan yana da muhimmanci. To amma kafin hakan wajibine mu jira sakamakon bincike, kafin mu yanke kudirorin da suka dace.

To shine har zuwa wane lokaci ne sojojin na Jamus zasu ci gaba da zama a Afghanistan karkashin rundunar kasa da kasa dake can. Shugaban gwmanati, Angela Merkel bata ce komai game da haka ba, ko da shike tace tana sa ran gwmanatin Afghanistan zata kara maida hankali ga matakan tsaron kasar ta da kanta.

Yayin da gwamanatin hadin gwiwa ta jam'iyun SPD da CDU da CSU ta daidaita a game da manufofn ta kan aiyukan sojojin Jamus a Afghanistan, ra'ayoyin yan adawa sun sha bam-bam. Jam'iyar nan ta masu neman canji, ta nemi janye sojojin ba tare da wani jinkiri ba. Shugaban jam'iyar Oskar Lafontaine yace ba zai yiwu Merkel tace Jamus bata wuce gona-da-iri ba.

Kakakin harkokin waje na jam'iyar Greens Jürgen Trittin yace babu wata manufa mai dacewa a game da kasar ta Afghanistan.

Yace gwmanatin bata cikin wani hali da zata iya horad da yan sanda da zasu kiyaye tsaro a kasar, kamar yadda Jamus din tayi wa kasashen duniya alkawari. Hakan yana nufin ana maganar tabbatar da tsaro kenan amma ba tare da an aiwatar dashi a zahiri ba.

Shugaban jam'iyar FDP Guido Westerwelle ya goyi bayan manufofin gwamnati kan kasar ta Afghanistan inda yace babu kasar da zata tura sojojin ta zuwa kasa kasa su fuskanci hadari in ba tare da wani dalili mai karfi ba.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Zainab Mohammed