1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta jaddada kudurin shawo kan sauyin yanayi

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel,ta jaddada cewa dole ne kasashe masu cigaban masana’antu da masu tasowa ,su taka irin tasu rawar adanagne da shawo kann matsalar sauyin yanayi.Merkel tayi wannan furucin ne ayayin da take shirin tafiya zauren mdd ,inda matsalar sauyin yanayi zai mamaye mahawarar shugabannin kasashen duniya.shjugabar gwamnatin na jamus ta jaddada cewa yana da matukar muhimmanci kasashe su cimma yarjejeniya domin samar da kariya,bayan yarjejeniyar Kyoto akan hayakin gas mai guba da masana’antu ke fitarwa,wanda waadinsa ke karewa a 2012.A halin da ake ciki yanzu dai a taron Montreal,wakilai daga kasashe wajen 200,sun cimma matsaya na rage hayaki mai gubana ,cikin gaggawa fiye da ainihin yadda aka shirya.