Merkel ta isa Liberiya a mataki na ƙarshe na rangadin Afirka | Labarai | DW | 07.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta isa Liberiya a mataki na ƙarshe na rangadin Afirka

Gwamnatin tarayyar Jamus ta yi amfani da ziyarar da shugabar gwamnati Angela Merkel ke kaiwa Liberia wajen ninka taimakon raya kasa da take bawa kasar dake yankin yammacin Afirka wadda yakin basasa ya yiwa kaca-kaca. Ministar ba da taimakon raya kasa ta Jamus Heidemarie Wieckzorek-Zeul wadda ke yiwa shugabar gwamnatin rakiya ta ce baya ga taimakon euro miliyan 14.4 da ta ware mata, Jamus ta sake ba da karin euro miliyan 4 don tafiyar da aikin sake gina hanyoyin sadarwa a Liberia. A yau dai ne Merkel ta isa birnin Monrovia a matakin karshe na rangadin wasu kasashen Afirka kudu da Sahara. Merkel zata gana da shugabar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf wadda ta yi mata gagarumar tarba a filin jirgin saman birnin Monrovia.