Merkel ta isa a birnin Pretoria a rangadin ƙasashen Afirka | Labarai | DW | 05.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta isa a birnin Pretoria a rangadin ƙasashen Afirka

A ci-gaba da rangadin kasashen Afirka da ta ke yi, SGJ Angela Merkel ta isa kasar ATK inda zata gana da shugaban kasa Thabo Mbeki a birnin Pretoria. Daga cikin batutuwan da zasu tattauna a kai har da shirye shiryen ATK na karbar bakoncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010. Merkel zata kuma kai ziyara a filin wasanni na Soccer City dake birnin Johannesburg. A jiya ta kammala ziyara a kasar Habasha inda ta yi jawabi a gaban wakilan KTA a birnin Addis Ababa. Shugabar gwamnatin ta Jamus ta yi kira da a karfafa huldodi tsakanin KTT da nahiyar Afirka sannan a girmama hakin bil Adama.