Merkel ta girgiza da kashe sojojin Jamus | Labarai | DW | 03.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta girgiza da kashe sojojin Jamus

Sojojin Jamus guda uku suka rasa rayukansu a yankin arewacin Afghanistan

default

Gwamnan lardin Kunduz dake Afganistan ya sanar da cewar sojojin Jamus sun kashe jami'an sojin ƙasar guda shida bisa ga kuskure. Hakan ya auku ne bayan  Jamusawan sun rasa uku daga cikin sojojinsu a musayar wuta a yankin arewacin Aghanistan din. Gwamnan Kunduz Mohammad Umar yace, sojin Jamus ɗinb sun buda wuta ne akan motar dake ɗauke da takwarorinsu na Afganistan a gunduwar Chardara a daren jiya.

Hari  na jiya akan dakarun Jamus dai ya girgiza  shugabar gwamnatin Angela Merkel. Rahotanni na nuni da cewar kimanin mayakan Taliban 100, suka yiwa dakarun Jamus dake aikin hakar binnannun nakiyoyin kwanton ɓauna, inda suka kashe uku tare da raunana wasu 8, a kusa da lardin na Kunduz dake arewacin Afganistan.

Mawallafiya: Zainab Mohammed. Edita: Yahouza Sadissou