1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta fara wata ziyarar ba zata a Afghanistan

November 3, 2007
https://p.dw.com/p/C156

SGJ Angela Merkel ta isa a birnin Kabul a wata ziyarar ba zata ta farko da ta kaiwa Afghanistan. A saboda dalilai na tsaro ba´a ba da labarin ziyarar ta ta ba sai bayan isarta kasar ta Afghanistan. Merkel zata gana da shugaba Hamid Karzai inda zasu tattauna akan halin da ake ciki a kasar. A karshe zata kai ziyara a hedkwatar sojojin Jamus dake aiki karkashin lemar rundunar ISAF a yankin Mazar-i-Sharif. Jamus dai ta girke sojoji kimanin dubu 3 wadanda ke tafiyar da aikin sake gina Afghanistan.