Merkel: Sabuwar dokar sajewar baki gagarumin cigaba | Labarai | DW | 25.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel: Sabuwar dokar sajewar baki gagarumin cigaba

Gwammatin Tarayyar Jamus ta amince da sabuwar dokar da za ta gaggauta sajewar baki a kasar.

Deutschland Kabinettsklausur Meseberg PK Sigmar Gabriel und Angela Merkel

Sigmar Gabriel da Angela Merkel bayan taron gwamnatin kawance a garin Meseberg

A gun wani babban taron da ta yi gwamnatin kawancen Tarayyar Jamus ta amince da daftarin dokar da ta tanadi sajewar baki a kasar. Karkashin dokar za a gaggauta shigar da 'yan gudun hijira a kasuwannin kwadagon kasar daidai wa daida. A bangare daya kuma akwai barazanar rage kudin tallafi ga wadanda suka ki yin biyayya ga matakan sajewar ba tare da wasu kwararan hujjoji ba. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana dokar da wani mataki na tarihi.

"A gani na gagarumin cigaba ne yadda gwamnatin tarayyar ta amince da dokar sajewar baki da za ta tallafa sannan a lokaci guda za ta bukaci su ma bakin su ba da ta su gundunmawa. Dokar za ta ba wa wadanda suka yi hobbasa damar cigaba da zama a Jamus."

Shi kuma mataimakin shugabar gwamnati Sigmar Gabriel ya kwatanta daftrin dokar da matakin farko kan turbar samun wata dokar yin ci-rani a Jamus.