Merkel na ziyarar aiki a Turkiya | Labarai | DW | 02.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel na ziyarar aiki a Turkiya

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na wata ziyarar aiki a Turkiya inda ta tattauna batutuwan da suka hada da na 'yan gudun hijira da na yaki da ta'addanci da Shugaba Erdogan.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta isa a wannan Alhamis a kasar Turkiyya a wata ziyarar aiki da ta kai a kasar. A lokacin ziyara wacce ta zo a daidai lokacin da ake zaman doya da man ja tsakanin Jamus da Turkiya, shugabar gwamnatin ta Jamus za ta gana a yammacin wannan Alhamis da shugaba Erdogan ,kana da firaminista Binali Yildimir kafin daga karshe ta gana da wakillan jam'iyyun adawar kasar. 

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta Turkiya ta fitar ta bayyana cewar ko baya ga batun yarjejeniyar da ta hada Ankara da Kungiyar Tarayyara Turai ta EU kan batun 'yan gudun hijira, shugabar gwamnatin ta Jamus da shugaba Erdogan za su kuma tattauna batun yaki da ta'addanci da na rikicin kasar Cyprus da kuma musamman batun huldar dangantakar Turkiya da kasashen Turai. Dangatakar kasashen biyu dai Turkiyya da Jamus ta tabarbare a sakamakon take-taken hakkin bil'Adama da kamen 'yan adawa da ya biyo bayan yUnkurin juyin mulkin da aka yi a kasar ta turkiya da bai kai ga yin nasara ba.