Merkel na son ′yan Tunisiya su koma gida | Labarai | DW | 14.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel na son 'yan Tunisiya su koma gida

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na cigaba da yin matsin lamba kan hukumomin Tunisiya don su kara matsa kaimi wajen kwashe 'yan kasarsu da suka gaza samun mafaka Jamus.

A wani taron manema labarai da ta yi da firaministan Tunisiya Youssef Chahed, Merkel ta ce a bara 'yan Tunisiya 116 ne kawai aka kwashe daga Jamus bayan da kasar ta ki amincewa da bukatarsu ta samun mafaka, adadin da Merkel din ta ce bai taka kara ya karya ba in aka yi la'akari da yawab 'yan Tunisiya din da ke neman mafaka a Jamus.

Wannan ne ya sanya Merkel shawartar hukumomin Tunisiya din da su kara azama wajen ganin an kwashe mutanen, har ma share guda ta tayin bada wani abu ga mutanen domin zaburar da su don su koma kasarsu ta asali.