1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabanin ra'ayin Merkel da Trump kan Pyongyang

Gazali Abdou Tasawa
September 20, 2017

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ba ta goyon bayan matakin Amirka na neman yin amfani da matakan soja wajen shawo kan rikicin nukiliyar Koriya ta Arewa.

https://p.dw.com/p/2kOnR
Deutschland wählt DW Interview mit Angela Merkel
Hoto: DW

Ta bayyana hakan ne a wata fira ta musamman da ta yi da tashar DW a wannan Laraba a ci gaba da tattaunawar da tashar take da shugabannin 'yan siyasar kasar ta Jamus a daidai lokacin da ake shirin gudanar da babban zabe a kasar inda ta ce hanyar diplomasiyya da ta matakin saka takunkumi su ne hanyoyi mafi a'ala wajen shawo kan wannan rikici. 

Da kuma ta juya kan batun siyasar kasar Jamus musamman dangane da batun jam'iyyar AfD ta masu kyamar baki da wasu rahotanni ke cewa na kara samun magoya baya daga jam'iyyu masu mulki, Angela Merkel cewa ta yi:

"Kan wannan batu amsa ta a bayyane take cewa ni abin da ya dame ni shi ne shawo kan matsalolin jama'a a fannin kiwon lafiya da ilimi da kuma dagewa a kan kawo karshen halayen kyama da na tarzoma."

 A ranar Lahadi mai zuwa ne dai ake gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar ta Jamus, inda shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ke sake tsayawa neman shugabancin gwamnatin kasar a karo na hudu.