Merkel: Dangantakar Turai da Amurka | Labarai | DW | 21.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel: Dangantakar Turai da Amurka

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta lashi takobin cimma daidaito da sabon shugaban Amurka kan wasu muhimman batutuwa da suka hadar da kasuwanci da sashin tsaro.

Ta kara da cewar za ta tabbatar da dorewar kyakkyawar dangantaka da ke tsakanin Turai da Amurka.

A wani mataki na martani dangane kalaman Trump na sa fifiko kan Amurka, Merkel ta ce, ya fayyace abun da gwamnatinsa zata fi mayar da hankali akai, lokacin jawabinsa na karbar madafan iko.

Sai dai ta jaddada muhimmanci samun hadin kai, domin aiki tare bisa ga tsarin doka da darajawa matakin hadin gwiwa a fannin tattalin arziki na duniya.

Shi kuwa shugaban Rasha Viladimir Putin, bayyana fata ya yi na tattauna muhimman batutuwa da gwamatin Donald Trump.