Merkel da yan majalisarta sun kammalla taron yini biyu | Labarai | DW | 24.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel da yan majalisarta sun kammalla taron yini biyu

Shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel da yan majalisarta sun kammala tattaunawar yini biyu adangane da manufofin gwamnatin a sauran shekaru biyu na waadinta akan karagar mulki.A jiya dai gwamnatin hadin gwiwar ta cimma madafa guda dangane da batutuwan makamashi,adangane da matsaloli na sauyin yanayi.An dai cimma matsaya guda tsakanin jamian manyan jammiiyun biyu ne,bayan tabka mahawara tssakaanin ministan kulaa da muhalli Sigmar Gabriel na jammiiyyar SPD da ministan harkokin tattali na jamiyyar yan mazan jiya ,Michael Glos.Gwamnatin dai ta cimma amincewa da rage hayakin gas da masanaantu ke fitarwa da wajen kashi 35 daga cikin 100,nan da shekara ta 2020.