1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel da Putin sun tattauna

Yusuf Bala Nayaya
May 11, 2018

Tsamin dangantaka tsakanin Amirka da Turai musamman bayan da Amirka ta fita daga yarjejeniyar da suka kulla ta nukiliyar Iran wani abu ne da zai kara sanya fahimtar Rasha da kasashen na Turai.

https://p.dw.com/p/2xYtJ
Angela Merkel und Wladimir Putin Kombobild
Hoto: picture-alliance/dpa/Gambarini/Druzhinin

Me ba da shawara ga Shugaba Vladimir Putin kan harkokin kasashen waje Yuri Ushakov ya ce Shugaba Putin ya tattauna ta wayar tarho da Angela Merkel shugabar gwamnatin Jamus kan yarjejeniyar da aka kulla da Iran a shekarar 2015 kuma matsayarsu guda daya ce. Lamarin da ke kara nuna kama hanyar fahimtar juna a cewar Ushakov.

Ushakov ya kara da cewa Putin zai kara tattaunawa da Merkel da ma Shugaba Emmanuel Macron nan gaba cikin wannan wata. Merkel za ta kai ziyara Rasha a ranar Juma'a me zuwa yayin da shi kuma Shugaba Macron zai gana da Putin a taron harkokin kasuwanci a St. Petersburg mako guda bayan ganawa da Merkel.