1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel a Poland

December 2, 2005

Shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel, ta kai ziyara a kasar Poland, a karo na farko tun da hau wannan mukamin. Za ta yi shawarwari da shugabannin kasar Poland a kan batutuwa da dama da suka sahfi huldodin dangantaka tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/Bu3k
Merkel
MerkelHoto: AP

Ministan harkokin wajen kasar Poland, Stefan Meller, ya bayyana cewa babu shakka kasarsa na ba da matukar muhimmanci ga ziyarar da shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel za ta kawo wa kasarsa:-

„Na yi imanin cewa, halin da ake ciki yanzu na ba mu karfin gwiwar huskantar makomarmu da kyakyawar manufa. Mun dai cim ma nasarori da dama a cikin shekarun 1990. Kuma muna sane da matsalolin da suka kunno kai a cikin shekarun baya. Ina dai kyautata zaton cewa, a cikin gwamnatin Jamus ta yanzu, akwai mutane da dama wadanda a karo farko za su iya fahimtarmu sosai, saboda muna da wasu dalilan tarihi da na siyasa na bai daya, wadanda suka hada mu.“

Ita dai kasar Poland, ba ta ji dadin hulda da gwamnatin shugaba Schröder ba, musamman ma dai saboda abin da take gani kamar ya fi ba da muhimmanci ga dangantakarsa da shugaba Putin na Rasha. A daya bangaren kuma, akwai wasu jam’iyyun kishin kasa na Poland din, wadanda ke ta yada kalamun nuna kyama ga Jamus, a cikin manufofinsu na yakin neman zabe. A halin da ake ciki yanzu dai, shugaban kasar Poland mai jiran gado, Lech Kaczynski, wanda a tsakiyar watan Disamba ne zai fara aikinsa, ya bayyana cewa zai fi mai da hankalinsa a tattaunawar da zai yi da Merkel ne, a kan matsaloli guda 3. Bisa cewarsa dai:-

„Da farko batun cibiyar tunawa da `yan koran nan da za a gina a Berlin. Na biyu kuma, shi ne batun taimakon da Jamus ke son bai wa `yan kabilun Jamusawa da ke zaune a arewaci da kuma yammacin yankunna kasarmu, ba tare da `yan kasar Poland da ke zaune a wannan yankin su ma sun ci moriyar wannan tallafin ba. Na uku kuma, shi ne, har ila yau dai, mun dage kan cewar bututun hayakin gas din nan da za a shimfida karkashin tekun Gabas, wanda zai taso daga Rasha zuwa Jamus, wata barazana ce ga maslahar kasar Poland.“

Shi ko Firamiyan Polan din, Kazimierz Marcinkiewicz, ya ce zai tunasad da shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel ne, da alkawarin da ta yi a lokacin yakin neman zabe, na cewa idan ta hau karagar mulki, ko yaushe sai gwamnatinta ta tuntubi Poland kafin ta tsai da wata muhimmiyar shawara a kan siyasar nahiyar Turai. Ana dai kyautata zaton cewa, a nata bangeren, Angela Merkel ma za ta nanata kin amincewar Jamus ne, ga shawarar nan ta radin kai da Poland din ta yanke, ta bai wa Amirka izinin kakkafa sansanonin makaman kariya da rokoki a harabarta, abin da ya saba wa manufofin tsaro na kungiyar Hadin Kan Turai, wadda ita kasar Poland din ma ke cikinta.

Ganawar da shugaban kasar Poland mai jiran gado, Lech Kaczynski, zai yi da Angela Merkel na da muhimmanci kwarai, saboda shugaban mai shekaru 56 da haihuwa, wanda kuma rikakken dan mazan jiya ne, ya ce a duk tsawon rayuwarsa bai taba sa kafarsa a Jamus ba.