Merkel a majalisar Turai | Siyasa | DW | 13.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Merkel a majalisar Turai

Shugabar gwamnatin Jamus ta gabatar da jawabi karo na biyu ga majalisar Turai

Angela Merkel

Angela Merkel

Shugabar gwamnatin ta Jamus, wadda bata dade da dawowa daga ziyarar Yankin Gabas ta Tsakiya ba tayi kira ga kasashen Turai da su karfafa goyan bayansu ga hada-hadar sasanta rikicin yankin gabas ta tsakiya. Sannan kamata yayi a yi koyi da irin ci gaban da kasashen Turai suka samu a kokarin hade kansu karkashin tutar kungiyar tarayyar Turai bayan kawo karshen yakin cacar baka tsakanin kasashen gabaci da na yammacin nahiyar. Merkel ta kara da cewar:

1.O-Ton

“Irin abin mamakin da ya faru a garemu a zamanin baya-bayan nan, kamata yayi ya zama mai ba mu kwarin guiwa a game da yiwuwar afkuwar hakan a wasu sassa na duniya. Wajibi ne babbar manufarmu da kasance ta samar da kasashen biyu na Isra’ila da Palasdinu da zasu zauna kafada-da-kafada da juna a cikin lumana da kwanciyar hankali da yalwa, saboda mu kanmu mun nakalci cewar akwai yiwuwar abopkan gaba su wayi gari suna kawance da juna.”

Jamus, a matsayinta na mai shugabancin kungiyar tarayyar Turai, ita ce zata wakilci kasashen Turai a taron kasa da kasa akan yankin gabas ta tsakiya da za a fara a Berlin mako mai zuwa. Mutane a wannan yanki na bukatar ganin nahiyar Turai ta taka muhimmiyar rawa kuma sun damu matuka ainun a game da shirin nukliyar kasar Iran, in ji Merkel, wadda a daya hannun kuma ta janye daga adawa mai tsananin da take yi da manyan manufofin hukumar zartaswa ta kungiyar tarayyar Turai a game da kare makomar yanayi. A yanzu Jamus din ma dai tana neman zama ja gaba ce a wannan manufa bayan da ta amince da ta kayyade yawan gubar carbondixide mai haddasa dimamar yanayin a cikin shekaru biyar masu zuwa. A cikin jawabin nata Merkel karawa tayi da cewar:

4.O-Ton

“Wajibi ne nahiyar Turai ta zama ja gaba akan wannan manufa. A ganina wannan abu ne da ya kamata mu wajabta wa kanmu. Amma kuma wajibi ne nahiyar Turai ta bayyanar a fili cewar babu wata matsalar dake nuna cewar duniyar duk jirgi daya ne ke dauke da mu kamar matsalar kare makomar yanayi kuma matakai da wata nahiya daya zata dauka ita kadai ba zasu taimaka a kawar da barazanar da dan-Adam ke fuskanta game da makomar rayuwarsa a doron kasa ba.”