1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

170808 Merkel Georgien

Hartbrich, Esther Tiflis WDR August 18, 2008

Merkel ta goyi da bayan ɗaukar Georgia a cikin ƙungiyar NATO

https://p.dw.com/p/Ezcd
Merkel da shugaba Saakashvili a TibilisiHoto: AP


Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nuna goya bayanta ga muradin Georgia na samun wakilci a cikin ƙungiyar ƙawance ta NATO. A ziyarar da ta kai birnin Tibilisi a ƙoƙarin gamno bakin zaren warware rikicin yankin Caucasus Merkel ta goyi da bayan shugaba Saakashvili inda ta alƙawarta tallfawa Georgia na sake gina ƙasar.


Shugaban Georgia Mikheil Saakashvili ya godewa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel dangane da ziyarar da ta kai birnin Tibilisi da cewa wani mataki ne na diplomasiya mai ƙarfafa guiwa.


Ya ce "Muna godiya da wannan ziyara ta shugabar gwamnatin Jamus, muna kuma godiya da matsayin da ta ɗauka a cikin kwanakin nan da kuma ƙoƙarin hana aukuwar abubuwan da suka auku."


A nata ɓangare Merkel ta jaddada taimakon Jamus ga Georgia. Kamar a lokacin ganawarta da shugaban Rasha a ranar Juma´a, a wannan karon ma ta sake nanata Georgia a matsayin ´yantacciyar ƙasa da ya zama wajibi a girmama ta kamar sauran ƙasashe.


Ta ce "Mun goyi da bayan shirin tsagaita wuta mai rukunai guda shida saboda haka muna sa rai za a gaggauta aiwatar da wannan shirin da aka sanyawa hannu."


A halin da ake ciki shugaban Rasha Dimitri Medvedev ya ce daga yau Litinin zai fara janye dakarunsa daga Rasha to sai dai za a ɗauki kwanaki masu yawa kafin dubban sojojin da motocin yaƙi sun kammala janyewa daga yankin ƙasar Georgia. Merkel ta yi nuna da abin ya da ya kamata a yi bayan janye sojojin na Rasha.


Ta ce "Ya kamata a gaggauta tura jami´an sa ido na ƙasa da ƙasa a wannan yanki. Shi ma shugaba Medvedev ya alƙawarta haka, bai kamata a samu wani jinkiri ba. Ana buƙatar kai taimakon jin ƙai ga ´yan gudun hijira musamman a yankin Ossetia ta Kudu sannan a yi musu tanadin komawa gida."


Ƙungiyar tarayyar Turai da Jamus sun nuna shirin ba da gudunmawa a shirin tura dakarun kiyaye zaman lafiya na ƙasa da ƙasa, inda Merkel ta alƙawarta ba da taimkon kuɗi don sake gina Georgia, sannan kuma Georgia ta na iya zama memba a ƙungiyar ƙawance ta NATO idan ta na so za a ci-gaba da shirye shiryen ɗaukarta cikin ƙungiyar kamar yadda aka fara.

Har yanzu shugaban Georgia Saakashvili ya dage cewa tun ba yau ba Rasha ta shirya mamaye ƙasarsa, amma ya musanta rawar da ƙasarsa ta taka wajen iza wutar wannan rikici. Da ma dai an ce laifi tudu ne ka taka naka kan hango na wani.