Menene yake haddasa taruwar dauɗar kunne | Amsoshin takardunku | DW | 02.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Menene yake haddasa taruwar dauɗar kunne

Bayani game da abin da ya sa dauɗar kunne take taruwa

default

Hoton kunne

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malama Zuwaira Haruna daga birnin Lome a ƙasar Togo. Malamar tana tambaya ne akan cewa; shin wai me yake haddasa taruwar dauɗar kunne, kuma shin dagaske ne wannan dauɗa tana da amfani ga kunnen ɗan Adam. Har ila yau ina so ku bani shawara akan yadda ya kamata na riƙa goge kunnena.

Amsa: To dangane da amsar wannan tambaya, daga nan Bonn Abba Bashir ya tuntuɓi Dr. Auwal Ibrahim Yola, Likita a Asibitin cututtuka masu saurin yaɗuwa da ke jihar Kanon Tarayyar Najeriya. Inda ya fara da tambayarsa ko menene yake haifar da dauɗar kunne?

Dr. Yola: Dauɗar kunne wani daskararren ruwa ne da wasu halittun kunne suke samarwa, kuma dama fatar jikin ɗan Adam cike take da ƙwayoyin halittu waɗanda aikinsu shi ne fitar da abubuwa daban-daban daga jikin ɗan Adam, irin su gumi da gishirin hanci da dai sauransu. Kuma wannan dauɗa ta kunne da ake gani tana daga cikin wata tsararriyar hanya da Allah maɗaukakin Sarki ya tsara, ta yadda kunne zai riƙa tsabtace kansa da kansa.

Bashir: Dr. Shin wannan dauɗa ta kunne tana da wani amfani ne ga Mutum?

Dr. Yola: E ƙwarai kuwa, dauɗar kunne tana hana datti ko ƙwayoyin cuta masu bin iska su shiga cikin kunne. Har ila yau kuma tana kare kunne daga ƙwari ko ƙudaje waɗanda za su iya tashi su faɗa cikin kunnen Mutum. Saboda haka babban amfanin wannan dauɗa ta kunne shi ne bayar da kariya ga halittun cikin kunne daga dukkan wani abu da ka iya faɗawa cikin kunnen.

Bashir: Waɗanne matsaloli kuma dauɗar kunne za ta iya haifarwa.

Dr. Yola: Dauɗar kunne za ta iya haifar da matsaloli irin su rashin jin sauti sosai yadda ya kamata da ciwo da kuma tari a wasu lokuta. Shi rashin jin sauti yana samuwa ne idan dauɗar kunne ta toshe ƙofar kunne gabaɗaya. Shi kuma jin ciwo yana aukuwa ne idan dauɗar kunne ta daɗe wanda ya sa har ta fara ɗaɗe fatar kunne. Shi kuma tari yana samuwa ne kasancewar waɗansu jijiyoyi na kunne sun haɗu da jijiyoyin maƙogwaro, to anan idan an samu matsala ko yaya dauɗar ta sulluɓe zuwa maƙogwaro sai hakan ya haifar da tari.

Bashir: Yaya ya kamata Mutum ya goge kunnensa?

Dr. Yola: Mutum zai iya amfani da abin goge kunne mai inganci. Wato tsinken nan mai auduga a jiki, saboda haka yin amfani da shi babu laifi in dai za a yi yadda ya dace, kuma dole a yi taka tsan-tsan don kada audugar ta maƙale a cikin kunnen. Kuma abu mafi alheri na tsare lafiyar kunne shine a goge iya wajen kunne da kuma ‘yar ƙofar cikin kunne kawai. Amma goge can cikin kunne yana da hatsari ƙwarai.

Bashir: Saboda me goge cikin kunne yake da hatsari?

Dr. Yola: Akwai dalilai uku da suka sa goge can cikin kunne yake da hatsari. Na farko dai, idan Mutum ya tara dauɗar kunne da yawa a kunnensa, to cusa abin goge kunne can ciki zai daɗa danna dauɗar ta danƙare a cikin kunnen mai makon ya naɗo ta waje. Wanda haka zai iya sa ƙaramar toshewa ta zama toshewa ta gabaɗaya. Na biyu, danna magogin kunne can ciki zai iya yin illa ga tantanin dake can cikin kunne, wata ƙila ma ya huda shi , kuma hakan zai haifar da mummunar illa ga kunne. Na uku, idan Mutum garin danna magogin kunne sai ya kuje kunnen daga can ciki, hakan zai iya sa ƙwayoyin cuta su shiga cikin kunnen. Amma dai babbar shawara ita ce , mutum ya guji danna magogi cikin kunne, domin ita wannan dauɗar ta kunne tana fitar da kanta daga cikin ramin kunne, kuma tana yin hakanne ba tare da neman taimakon kowa ba. Kuma ma dai me yai zafi, a tuna fa dauɗar kunne tana kare halittun cikin kunne daga samun lahani.

Bashir: To yaya Mutum zai yi da matsalar dauɗar kunne idan ta same shi?

Dr. Yola: Mutanen da suke da matsala ko kuma lalurar kunne ya kamata su ziyarci likitan kunne. Amma kada Mutum ya ce zai yi maganin matsalar dauɗar kunne da kansa.