1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Menene matsayin zakkar fidda kai

Abba BashirOctober 8, 2007

Bayani akan matsayin Zakkar fidda kai

https://p.dw.com/p/BvUf
Abinci a Ramadan
Abinci a RamadanHoto: AP

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Yahuza: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malama Bilku Abbas daga Birnin Zariya a Najeriya; Malamar tana tambaya ne game da matsayin zakkar fidda kai?

Bashir: To na mika wannan tambaya ga Shahararren malamain addinin musuluncin nan dake jihar kanon tarayyar Najeriya, wato Dr Aminuddeen Abubakar, Ga kuma abin da ya ce game da amsar wannan tambaya.

Aminuddeen: Zakkar fidda kai sunna ce daga cikin sunnonin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam. Hakika manzon Allah ya fitar da zakkar fidda kai, kuma sahabbansa masu albarka sun aikata hakan, kamar yadda manzon Allah ya yi.

Za’a iya fitar da wannan zakka, kafin ganin watan shawwal da kwana biyar (5) Zuwa goma (10), domin sahabbai sun aikata haka.Amma zance mafi shara shine, ana fitar da ita ranar Sallah kafin a tafi Idi. Haka kuma ana fitar da zakkar ga kowane musulmi; Yaro da Babba, Mace da Namiji, Da da Bawa, kuma ana fitarwa ko wanne mutum mudannabi hudu, ko kuma ace kilo biyu da rabi (2.5 Kg). Amma abin mamaki wasu mutanen duk da cewar suna da hali basu damu da fitar da zakkar ba, saboda a ganinsu suma talakawa ne da ya kamata a baiwa zakkar.

Lallai ne a fitar da zakkar tun kafin a tafi sallar Idi. Duk mutumin da ya bari aka sakko daga Sallar Idi bai fitar da zakkar ba, to hukuncin zakkar sa ya koma kamar sauran sadaka, wato ba zakkar fidda kai bace. Sai dai idan bisa larura ne to wannan babu komai.

Ya kamata yan-uwa su fahimci cewa, hikimar fitar da zakkar fidda kai ranar Idi kafin a tafi filin Idi shine, domin a baiwa mabukata don kada su yi bara ranar Idi. Saboda rana ce ta murna da farinciki da ci da sha da ziyara, don haka bai kamata a yi bara a wannan rana ba.

Allah ya sa mu dace.