1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Menene ma’anar RSVP

Abba BashirJanuary 31, 2006

Bayani game da ma’anar RSVP

https://p.dw.com/p/BvVa
Katunan gayyata
Katunan gayyataHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon, tafito ne daga hannun Malam Attahiru, mazauni a Birnin Yamai, dake Jamhuriyar Nijer.Malamin ya ce don Allah yana so a sanar da shi ma’anar haruffan nan gada hudu wato RSVP.

Amsa: To a kokarinmu na lalubo amsar wannan tambaya ta malam Attahiru, mun binciki hanyoyi da dama ind muka ci karo da cewar, akwai ma’a noni da dama da suke damfare da wadannan haruffa guda hudu na RSVP,ya dai danganta da irin sigar da haruffan suka zo.

Binciken da muka yi ta na’ura mai kwakwalwa, ya nuna mana cewar a cikin gizagizan sadarwa na Duniya mai kula da takaitattun kalmomi,akwai ma’anoni 31 na wadannan haruffa guda hudu wato RSVP.Amma dai duk da haka a cikin wannan shafin an nunar dacewa ma’anar da aka fi sani , kuma aka fi amfani da ita, itace Kalmar Faransanci ta“Repondez S’il Vous Plait’’ wato ma’anar ta a Haussance itace, ka ba da amsa don Allah.

To sabodahaka idan Malam Attahiru yana nufin takaitattun kalmomi guda hudu na RSVP wadanda ake rubutawa a karkashin katin gayyata, tosai muce dashi wadannan haruffa suna nufin,Mutumin da aka gayyata ya sanar da wanda ya gayyace shi cewar, ya amsa gayyatar ko kuma bai amsa ba,wato zai samu damar halarta ko kuma bazai samu damar halartar gayyatar da aka yi masa ba. Shi yasa ma akarkashin haruffan zaka ga ana rubuta adireshi ko kuma lambar wayar tarho da za’a bayar da amsa.

A wani lokaci akan hada RSVP da “Regrets only’’, to yin hakan a tsarin nahawu kuskurene,domin a yayin da RSVP ke nufin, a bada amsa don Allah, ita kuwa Regrets only na nufin, idan baza ka samu damar halarta ba to ka sanar, wato dai a takaice ma’anar ta itace, Idan ba zaka zo ba ka sanar. Sabodahaka kenan kowanne cin gashin kansa ya keyi, sai dai a zabi daya a yi amfani da shi, ba duka biyun a lokaci daya ba.

Haka zalika hada kalmar Please da RSVP a lokaci guda kuskure ne, wato dai kamar haka “Please RSVP’’. Domin kuwa “Please’’ a Hausance ta na nufin (Don Allah),RSVP kuma, (ka ba da amsa don Allah), wato kenan idan Mutum ya hada duka biyun a waje guda, kamar ya ce ne, Don Allah ka ba da amsa don Allah, yi hakan kuwa maimaita abu daya ne.