1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Menene ma’anar Photosynthesis

Bayanin game da ma’anar Photosynthesis

tsirrai

tsirrai

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Yahaya Aminu daga Jihar kanon Tarayyar Najeriya; Malamin cewa yayi; Ni dai Dalibi ne a makarantar Sakandare, to a makarantar mu , a darasin Ilimin halittu wato Biology, an sanar damu wani abu da ake kira “Photosynthesis’’. Na yi matukar kokarina domin malamin ya yi min bayanin wannan abu da hausa yadda zan fahimta, amma abin ya gagara. Shi yasa na yanke shawarar rubuto muku ina mai rokon ku da ku yi min bayani cikakke akan ma’anar “Photosynthesis’’

Amsa: To da farko dai kafin a fahimci ma’anar Photosyntesis kai tsaye ya kamata a fahimci cewa;Tsirrai na taka muhimmiyar rawa wajen kawata duniya da kuma sanya ita Duniya din a matsayin wani mazauni da za’a iya rayuwa. Sune suke gyara mana iska, suke zaunar da yanayin sararin sama da daidaita kadawar iska a sararin Duniya. Iskar Oxygen da muke shaka tsirrai ne suke samar da ita. Muhimman abincin da muke ci sune suke samarwa.

Sunadaran gina jikin su kansu tsirran suna fitowa ne ta wani tsari na musamman a cikin kwayoyin jikinsu wanda ta nan ne dukkan komai nasu yake fitowa.

Kwayoyin tsirrai, sabanin na mutane da dabbobi, suna iya aiki kai tsaye ne da hasken Rana. Sai su mayar da sunadaran da suka diba daga rana zuwa kwayoyi su taskace su a jikinsu ta wata irin tsari na musamman. Wannan tsari shine ake kira “photosynthesis”.

Hakika, wannan tsari yana tafiya ne ba ta wadannan kwayoyin ba amma ta chloroplast, da wasu gabbansa da suke bawa tsirran koren launi. Wadannan kananan korayen gabbai ana iya ganinsu ne ta cikin na’urar hangen nesa, kuma sune kadai a fadin duniya suke iya taskace hasken rana a cikin kwayoyin halittar sunadaran.

Yawan adadin kwayoyin halittar da tsirran suke samarwa aban kasa ya kai tan biliyan 200 a shekara. Wannan samarwa na da matukar amfani ga dukkan ababan halittar da suke raye aban kasa. Kuma ana riskar hakan ta wani hadadden tsarin sunadarai. Dubban kwayoyin “chlorophyll” dake cikin chloroplast sune suke lura da haske a dan kankanin lokaci, kusan kace dubbai a cikin sakan daya. Shi yasa abubuwa da yawa suke faruwa a cikin chlorophyll din ba’a iya sani da kuma gani.

Canza hasken rana zuwa nau’ra ko sunadarai wata sabuwar fasaha ce da ta bullo. Yadda ake yi kuwa, sai anyi amfani da manyan na’urori. Amma kalli kwayoyin tsirrai duk da kankantarsu wadda ta sa ba’a iya ganinsu da ido kiri da muzu, suna yin wannan aiki shekaru miliyoyi masu yawa. Wannan kyakkyawan tsari na nuna kasaitar halitta don kowa ya gani. Wannan hadadden tsari na photosynthesis kasaitaccen shiri ne wanda Ubangiji ya halitta. Masana’antar da babu irinta a Duniya, amma sai gata a dan karamin wuri a cikin ganyayyaki. Irin wannan tsari daya ne daga ayoyin da suke bayyana cewa dukkan ababan halitta, halittar Ubangiji ce, majibincin dukkan Duniyoyi.

 • Kwanan wata 14.08.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUk
 • Kwanan wata 14.08.2007
 • Mawallafi Abba Bashir
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUk