1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Menene hukuncin mutumin da yake cikin yin sahur aka kira Sallah

Abba BashirOctober 1, 2007

Bayani akan hukuncin mutumin da yake cikin yin sahur aka kira Sallah

https://p.dw.com/p/BvUg
Masallacin Birnin Berlin a Germany
Masallacin Birnin Berlin a GermanyHoto: dpa

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Abdullahi: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Dan’azumi Kabir daga Jihar Yobe a Najeriya,Malamin yana tambaya ne game da cewar; Shin idan mutum yana cikin yin sahur, sai ya ji kiran sallah, to yaya zai yi?

Bashir: To na mika wannan tambaya ga Shahararren malamin addinin musuluncin nan dake jihar kanon tarayyar Najeriya, wato Dr Aminuddeen Abubakar, Ga kuma abin da ya ce game da amsar wannan tambaya.

Aminuddeen: To idan mutum yana cikin yin sahursai ya ji kiran sallah, abin da zai yi shine, sai ya karasa cinye abincin da ke hannunsa. Dalili shine Hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam, wanda Abu Dawud ya ruwaito, wanda kuma aka karbo daga Abu huraira (Allah ya yarda da shi) ya ce: “Idan dayan ku ya ji kiran sallah alhali kwarya tana hannunsa, kada ya ajiye ta har sai ya biya bukatarsa’’.

To amma fa yan-uwa sai a yi hattara, kada mutum ya mayar da wannan dabi’a ta zama al’darsa ta yau da kullum.

Allah shine mafi sani.