1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Menene hukuncin mace mai shayarwa idan ta sha azumi

Abba BashirSeptember 25, 2007

Hukuncin mace mai ciki ko mai shayarwa wadda ta sha Azumi

https://p.dw.com/p/BvUh
Mace mai ciki da mijinta
Mace mai ciki da mijintaHoto: AP

Masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, sannunmu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardunku, shirin da a kowane mako yake amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.

Abdullahi: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malama Ramlatu Abdullahi daga Jihar Bauchi a Najeriya, Malamar cewa tayi; Menene hukuncin mace mai shayarwa idan ta sha azumi a watan ramadan?

Bashir: To da farko dai mace mai ciki ko mai shayarwa zata iya ajiye azumi idan tana tsoron cutuwarta ko cutuwar yaron da take shayarwa ko kuma na yaron dake cikinta idan ta yi azumin.

Dalili yana cikin Hadisin da aka ruwaito daga Anas dan-malik al-ka’abi (Allah ya yarda da shi), daga Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam ya ce: “Hakika Allah ya daukewa matafiyi rabin Sallah, kuma ya daukewa matafiyi da mai ciki da mai shayarwa azumi’’. Ibn Maajah ne ya ruwairo wannan hadisi. Haka kuma Abu dawud da Tirmuzi suma sun ruwaito wannan Hadisi.

Malamai sun yi sabani dangane da ramuwa ga mai ciki da mai shayarwa.Wadansu sun tafi akan fatawar Abdullahi Dan-umar da Abdullahi Dan-abbas da Ishaq bin Rahawaih cewa; mai ciki da mai shayarwa babu ramuwa akansu sai dai ciyar da miskini. Dalilinsu kuwa shine fadin Allah ta’ala: “Kuma akan wadanda suke yinsa da wahala, akwai Fansa; ciyar da miskini……..har zuwa karshen aya’’ kuma wannnan aya ta zo ne a cikin suratul bakara aya ta 184. Suka ce wannan ayar ta hada da tsofaffi da ba za su iya yin azumi ba, da mai ciki da mai shayarwa.

Haka zalika shaykh Nasiruddeen Albani a cikin littafinsa Irwaa al-Ghaleel, da kuma almajiransa a cikin littafin Sifatus-Saum-an-Nabiyi, sun tafi akan cewa fatawar bin Umar da bin Abbas babu wanda ya saba musu a cikin sahabbai, don haka za’a iya cewa kamar ijima’i ne na jamhurin sahabbai baki daya.

To sai dai jamhur na mafiya yawan malamai sun tafi akan cewa, mai ciki da mai shayarwa suna cikin marasa lafiya ne, don haka zasu rama azumin da suka sha mai makon ciyarwa. Wannan shine ra’ayin Imam Auza’i da Imam Hasanul Basari da Ibrahim an-Nakha’i da Ataa, da imamuz-zuhuri da kuma Imam Malik. Kuma wannan shine ra’ayin wadansu daga cikin magabata kamar su Ibn Taimiyya da almajiransa. Daga cikin malamai na kusa wadanda suka tafi akan wannan fahimta akwai ibn Baz da Al-uthaimin da sauransu.

Allah shine mafi sani.