Menene Bamuda Triangle | Amsoshin takardunku | DW | 11.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Menene Bamuda Triangle

Takaitaccen bayanin Bamuda Triangle

Tsibirin Bamuda

Tsibirin Bamuda

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon, ta fitone daga hannun Malam Aminu dogo direba layin maradi- kano, mazauni a maradi dake jamhuriyar nijer.Malamin ya na tambayar cewa,

Shin da gaske ne akwai wani wuri a wannan duniya ta mu , da ake kira da suna bamuda triangle , wanda duk abinda ya ratsa ta cikin sa sai ya halaka?

To shi dai wannan wuri da ake kira da suna bamuda triangle,wani yankine da ake siffanta shi da kusurwowi guda uku a cikin tekun atlantika´a kasar amurka, kuma yana nan ne a daura da kudancin gabar tekun, wanda ya hada da wani bangare daga tsibirin bahama da puerto-rico,da wani yanki na jihar florida, da kuma shi kansa tsibirin bamuda wanda wannan wuri ya samo sunansa daga gareshi.

Jiragen ruwa da kuma na sama da dama sun halaka sun bace bat sakamakon kokarin ratsawa ta wannan wuri na bamuda.Wata mujalla da ake kira da suna “national geographic magazine’’ ta bayyana wannan yanki na bamuda a matsayin alamari mafigirma kuma mafi rikitarwa da aka kasa fahimtarsa a wannan zamani

Akwai jirage da dama da suka halaka a wannan wu, misali a ranar 8 ga watan janairun 1962 wani jirgin sama da ake kira da suna aerial tanker kirar kb50 ya bace bat sakamakon bi ta sararin samaniyar wannan wuri, an kuma nemeshi ko sama ko kasa har yau baaji duriyarsaba.

Duk da cewa a wancan lokaci kafafen yada labarai da dama sun sun bayar da rahoton cewa wannan jirgi ya yi hadarine a sama sannan kuma ya fado ya nutse a cikin teku. Sai dai sakamakon cikakken bincike da aka gudanar ya musanta wadannan rahotanni na kafafen yada labarai, domoin kuwa babu wata hujja daya tilo da ta tabbatar da hakan. Kuma wannan ba ita ce bacewa ta farko kuma ta ban alajabi ba, domin kuwa tun kafin wannan ta auku akwai wadansu jiragen guda biyu da suka hadu da irin wannan garari.

Nafarko dai shine jirgi mai dauke da fasinja , kirara babban jirgi mai lamba 19 , wannan jirgi dai ya bace bat, sakamakon kokarn ratsawa ta sararin samaniyar wannan wuri na bamuda a shekarar 1945. sai kuma jirgi na biyu kirar nc16002mai dauke da kungiyar maaikatan jirgi wanda shi kuma ya hadu da nasa gararin bacewara shekarar 1948.

To akwai dai hasashe na mutane daga fannonin ilimi daban daban dangane da kokarin bayyana abinda ya ke a wannan wuri na bamuda.

Misali masana ilimin sinadarin da ke janyo abu daga sama zuwa kasa suna ganin cewa a wannan yankin na bamuda akwai wani mayan karfe na musamman wanda yake da karfin fizgo duk wani abu da ya yi kokarin ratsa wannan wuri komai girmansa kuwa. Kuma dazarar ya zukoshi tun da yake a tsakiyar teku ne to shi kenan shifa halaka ta gabbata a gareshi,kuma ba za’a taba jin duriyarsa ba .

Su kuwa masana ilimin falaki , suna ganin cewa, wannan wuri na bamuda da ke a cikin teku,wata kafa ce ta zuwa sauran duniyoyi, sabodahaka duk abin da ya bi ta cikinsa wato kamar dai ya tafi wata Duniyar ne ba ta Dan-adam ba .

Su kuma masana ilimin falsafa a nasu raayin, wurin na bamuda wata katafariyar fadar shedan ce , inda duk abin da yayi kokarin tsallakata zai halaka.

Wannan al’amari dai ba wai magana ce ta hadari ko tsautsayi ba , magana ce ta bacewa bat a nemi abu ko sama ko kasa a rasa , sabadahaka kenan batun sanin kididdigar yawan mutanen da suka halaka ko kuma yawan dukiyoyin da aka rasa abu ne mawuyaci.

Sai dai kawai maganar dai a nan itace cewar , wannan wuri da ake kira da suna Bamuda triangle gaskiya ne akwai shi,amma har yanzu Duniya bata tabbatar da ainihin ko menene a wannan wuriba.