Mene ne asalin dangantakar ƙasar Sin da tsibirin Taiwan | Amsoshin takardunku | DW | 14.07.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Mene ne asalin dangantakar ƙasar Sin da tsibirin Taiwan

Taƙaitaccen tarihin dangantakar ƙasar Sin da tsibirin Taiwa

default

'yan Taiwan suna zanga-zangar neman 'yancin kai daga ƙasar Sin

Don Allah ku ba ni tarihin dangantakar ƙasar Sin da tsibirin Taiwan.

Wannan ita ce tambayar da muka samu daga hannun Malama Amina Nuhu Ado daga birnin  Yamai na Jamhuriyar Nijer.


Taiwan wani yanki ne da ba za a iya raba shi da ƙasar Sin ba. Ilimin tarihin  ƙasa ya nuna mana cewa, a shekaru dubbai da suka wuce, Taiwan da babban yankin ƙasar Sin, haɗe suke da juna. Amma sakamakon wata mummunar girgizar ƙasa da aka yi a zamanin da, a wannan yanki da ya haɗa Taiwan da babban lardin ƙasar Sin, sai ya sa yankin ya zama wani mashigin teku, sakamakon hanka sai Taiwan ta tsinci kanta a matsayin wani tsibiri.

Kayayyakin tarihi masu yawan gaske, waɗanda suka shafi tsarin rayuwar al'umma, kamar kayan abinci , da tufafi da makwanci waɗanda aka samu sun bayyana cewa, ainihin al'adun mutanen Taiwan da na babban lardin ƙasar Sin da suka kasance a da, kafin a fara rubuta tarihi, duk ɗaya ne.

A ƙarshen ƙarni na 19, A shekarar 1894, ƙasar Japan ta haddasa yaƙi a tsakaninta da ƙasar Sin. Kuma A shekarar 1895, gwamnatin daular Qing ta kasar Sin wadda ta faɗi a wannan yaƙi ta sayar da mutuncin al'ummarta, sakamakon yarda da ta yi, na sanya hannu a kan yarjejeniyar Maguan. Bisa wannan yarjejeniya, ƙasar Japan ta sami ikon mulki kan tsibirin Taiwan da tsibiran Penghu. Ta haka Japan  ta shiga mulkin mallaka har na tsawon shekaru 50 a Taiwan.

A ranar 1 ga watan Disamba, 1944 a cikin Sanarwar Alƙahira wadda ƙasashen Sin da Amurka da Ingila suka kai ga cimma yarjejeniya, an tsai da ƙudurin cewa: Yankunan da ƙasar Japan ta karɓe daga ƙasar Sin, dole ne a komar da su cikin ƙasar Sin. In da kuwa hakan ya tabbata. Tsibirin Taiwan sai ya koma ƙarƙashin ƙasar Sin.

Tsibirin na Taiwan dai ya ɓalle daga ƙasar Sin a 1949 bayan yaƙin basasa, tun daga wancan lokaci zuwa yanzu take cin mulkin gashin kanta, duk da cewar Beijing na yi mata kallon wani yankinta ne da ya ɓalle, wanda kuma ya sa har yanzu take barazanar kai mata mamaye idan har ta sanar da 'yancin kai a hukumance.