MEND ta yi gargaɗin kai hari a Abuja | Labarai | DW | 16.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MEND ta yi gargaɗin kai hari a Abuja

Ƙungiyar dake iƙirarin kare yankin Niger Delta a Najeriya, ta yi gargaɗin cewa za ta kai wasu munanan hare-haren bama bamai a birnin Abuja.

default

'Yan bindigan ƙungiyar MEND

Ƙungiyar tsagerun yankin Niger Delta wato MEND wadda ta ɗauki alhakin kai hari a ranar bikin 'yancin kan ƙasar, ta ce ta shirya kai wasu sabbin hare-haren bama bamai a birnin Abuja. Ƙungiyar ta ce za ta kai harin domin ta wanke abokan adawan Goodluck Jonathan, waɗanda shugaban na Najeriya ya shafawa kashin kaji bayan harin na Abuja. Kakakin ƙungiyar Jomo Gbomo ya ce za mu ba da gargaɗi na mintuna 30 don kaucewa kisan fararen hula, sai mu ja gefe mu ta da bama baman, mu ga ko za'a sake shafawa wasu kashin kaji. A harin da ƙungiyar MEND ta kai a ranar bikin cika shekaru hamsin da samun 'yancin kan Najeriya, an hallaka mutane aƙalla 12 da raunata wasu da yawa, kuma daga bisani sai jami'an tsaro suka kama Reymon Dokpesi daraktan kamfen na ɗan takaran shugaban ƙasar Janar Ibrahim Babangida mai ritaya, wanda ya ce bana babu ja da baya sai ya ƙalubalanci Goodluck Jonathan. A jiya dai an rufe ɗaukacin hanyoyin da suka nufi dandalin Eagle Square dake Abuja, domin matar shugaban ƙasa na taro. Gbomo ya ce a wani yunƙuri na daƙushe duk wanda ke takara da shi, shugaba Goodluck Jonathan ya raɓe da batun ta'addanci, don yi wa abokan adawar sa bita da ƙulli.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammad Nasir Awal