Mece ce tiyatar (Autopsy) | Amsoshin takardunku | DW | 12.01.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Mece ce tiyatar (Autopsy)

Taƙaitaccen bayani game da tiyatar (Autopsy)

default

Likitoci na nazarin ƙodar wani mutum domin fahimtar dalilin mutuwar sa

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga Hannun Malama Magajiya Safiyanu daga Jihar Kano a Najeriya, Malamar cewa ta yi; Don Allah Sashen Hausa ku bayyana min ma'anar tiyatar nan da ake kira da suna (Autopsy), kuma ku sanar da ni dalilin da ya sa ake yin ta.

Amsa: Ita dai tiyatar (Autopsy) za a iya bayyana ta a Hausance da cewa Gani da ido maganin tambaya. Wato wata irin tiyata ce , ko kuma muce fiɗa ce ta musamman da ƙwararrun likitoci na musamman suke yi wa gawar mutum domin a gano gaskiyar yanayin da jikin mutum yake ciki a lokacin da yake raye tare kuma da gano abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Kamar yadda wani likita mai yin irin wannan fiɗa ya faɗa, anan Jamus wato Dr. Friedlander, ya ce akwai muhimman abubuwa da daman gaske dangane da wannan fiɗa ta Autopsy da ake yi. Kusan a kowane lokaci akwai abubuwa da iyalan mamaci suke ƙaruwa da su idan aka yi wannan fiɗa, ko da kuwa hukuma bata bayar da umarnin yin hakan ba. Ya ce daga cikin irin wannan fiɗa ta (gani da ido) guda 800 da ya yi, kusan a kowacce sai da ya samu wani sabon abu wanda ya kamata a ce an san shi a lokacin da mutum yake raye. Kuma ko da a manyan asibitoci, kashi ɗaya bisa hudu na irin wannan fiɗa da ake yi suna gano wata sabuwar cuta a jikin ɗan Adam, wadda kafin wannan lokaci ba a san wannan cuta ba.

Dr. Friedlander ya ce, babban burinsa ga irin wannan fiɗa da yake yi shi ne, baiwa iyalan mamaci gaskiyar bayanin da suke nema na sanadiyyar mutuwar ɗan uwansu. To ita dai irin wannan fiɗa ko kuma in ce tiyata da ake yi wa gawar mutum, a mafiya yawan dokokin ƙasashe; dole sai dai idan hukuma ce ta bayar da umarnin yin haka, to amma a wasu ƙasashen , iyalai ko masoya na iya tuntuɓar likitoci kai tsaye domin su yi irin wannan fiɗa.

Ita dai irin wannan fiɗa ana yin ta ne a mafiya yawan lokuta saboda wani abu da ya shafi shari'a ko kuma idan abu ne da ya shafi wata cuta da ta kashe mutum, wadda kuma kafin mutum ya rasu ba a iya gano cutar ba, to domin a gano ainihin cutar da ta kashe mutum sai a yi irin wannan fiɗa ta gani da ido. Sai dai a mafiya yawan lokuta idan hukumace ta bayar da umarnin yin wannan fiɗa, to za a tarar cewa, abu ne da ya shafi laifi, kamar su kisan gilla, ko kisan ganganci kodai wani kisa da ya shafi karya doka, ko take haƙƙin ɗan Adam. A wasu lokuta kuma daliban neman ilimi na likitanci sukan yi irin wannan fiɗa domin nazarin bincike akan wata cuta.