MDD:Ta ce ana cin zarafin bil Adama a Turkiyya
March 20, 2018Talla
A cikin wani rahoton da hukumar kare hakib bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta ce yanzu haka ana tsare da mutane kusan dubu 160 a gidajen kurkuku a tsawo watanni 18. Kana aka kori wasu ma'aikatan gwamnatin dubu 152 wadanda suka hada da malaman makaranta da alkalai da lauyoyi.