Mdd zata tallafawa Zimbabwe a fannin siyasa da tattalin arziki | Labarai | DW | 25.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mdd zata tallafawa Zimbabwe a fannin siyasa da tattalin arziki

Kasashen Africa ta kudu da kuma Biritaniya sun yi maraba da tayin Mdd na kokarin tallafawa kasar Zimbabwe, fita daga kunci na siyasa da tattalin arziki data fada a ciki.

Jim kadan bayan tattaunawar su a birnin London , shugaba Thabo Mbeki na Africa ta kudu da takwaran sa na Biritaniya, Mr Tony Blair sun yi fatan cewa wannan kokari da Mdd keyi kwalliya zata biya kudin sabulu.

Rahotanni dai sun rawaito magatakardar Mdd Kofi Anan na bayyana fatan sa na kai ziyara izuwa Zimbabwe nan bada dadewaba, to amma hakan a cewar Mr Anan zai tabbata ne kawai idan mahukuntan na Zimbabwe sun nuna amannar aiki da Mdd ta fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma gudanar da ayyukan agaji.