Mdd zata fadada aikin kiyaye zaman lafiya a Haiti | Labarai | DW | 16.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mdd zata fadada aikin kiyaye zaman lafiya a Haiti

Kwamitin sulhu na Mdd ya amince da kara wa´adin ci gaba da gudanar da aikkin kiyaye zaman lafiya da rundunar Majalisar keyi a kasar Haiti.

To sai dai kuma, Majalisar tace zata rage yawan dakarun sojin kiyaye zaman lafiyar dake kasar ta Haiti daga dubu 7 da dari biyar izuwa dubu 7 da dari biyu.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa an aike da tawagar kiyaye zaman lafiyar ta Mdd ne izuwa Haitin, don tabbatar da doka da Oda, bayan tunbuke shugaba Jean Bertrand Aristide daga mukamin sa na shugaban kasa.

Kasar dai ta Haiti ta fuskanci matsaloli ne na yawaitar kai hare hare da kuma garkuwa da mutane ne, a bayan da Shugaba Aristide ya bar gadon mulkin kasar.

Rahotanni dai sun nunar da cewa a yanzu rundunar sojin kiyaye zaman lafiya ta Mdd zata ci gaba da kasancewa a kasar ta Haiti daga nan har zuwa 15 ga fabarairun shekara ta 2007.