MDD za ta fara tura sojoji 3,500 zuwa Lebanon | Labarai | DW | 16.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD za ta fara tura sojoji 3,500 zuwa Lebanon

Majalisar ɗinkin duniya na shirin fara tura dakarun kiyaye zaman lafiya 3,500 zuwa Lebanon nan da makwanni biyu domin sa ido a kan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma. Majalisar ɗinkin duniyar na dora fata a kan Faransa na jagorantar dakarun soji. A yau laraba wasu manyan jamián sojin Faransa za su gana da jamián kiyaye zaman lafiyar na Majalisar ɗinkin duniya a birnin New York. ƙasashen turai da dama sun nuna aniyar su ta bada gudunmawar soji domin taimakawa wajen aikin kiyaye zaman lafiyar. Hadi Annabi jamiín majalisar ɗinkin duniya mai lura da aikin kiyaye zaman lafiya, yace ana buƙatar tura dakarun sojin cikin gaggawa domin cimma ƙudirin da majalisar ta zartar a makon da ya gabata. ƙudirin ya buƙaci tura dakaru 15,000 na gamaiyar ƙasa da ƙasa domin kare zaman lafiyar, sannan da janyewar sojin Israila daga yankin kudancin Lebanon.