MDD: Yunwa a sansanonin ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 02.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD: Yunwa a sansanonin 'yan gudun hijira

Yara kanana na fuskantar barazanar matsanancin yunwa da ka kai su ga halaka, a jihohin da rikicin Boko Haram ya ritsa da su a arewacin Najeriya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ninka yawan adadin kudin jin kai da yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ke bukata zuwa dalar Amurka biliyan daya. Za'a yi amfani da kudin ne wajen taimakawa kusan mutanme miliyan bakwai da rikicin Boko Haram ya ritsa da su.

Peter Lundberg da ke zama mataimakin kodinatan hukumar jin kai ta MDD ya sanar da cewar yara dubu 75 na fuskantar barazanar kamuwa da tamowa, wanda zai iya hallaka su cikin 'yan watanni masu zuwa, idan har ba'a kai musu dauki ba.

Kazalika manajan harkokin yada labaru na kungiyar agajin yara ta Save the children Dan Stewart, wanda ya ziyarci Maiduguri kwanakinnan, ya jaddada mawuyacin halin da mazauna sansanonin 'yan gudun hijira ke ciki.

"Akasari sun rasa duk abunda suka mallaka, don haka ba za su iya kula da kansu ba. Hakan na nufin akwai barazanar matsanancin yunwa a gaba. Akwai yara wajebn dubu 400 da zasu fuskanci karancin abinci mai razanarwa a shekara mai zuwa"

 

Mayakan fafutukar sun hallaka rayukan mutane dubu 15, tare da korar sama da miliyan biyu daga matsugunnensu, tun barkewar wannan rikici shekaru bakwai da suka gabata.