1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mdd tayi suka game da rataye mukarraban Saddam

January 16, 2007
https://p.dw.com/p/BuUK

Shugabar hukumar kare hakkin yan Adam ta majalisar dinkin duniya, Louis Arbor tayi suka a game da rataye mukarraban tsohon shugaban Irak, Saddam Hussein guda biyu da aka yi jiya da asuba a Bagadaza.

Loius Arbor taci gaba da cewa aiwatar da wannan mataki ka iya zama cikas a kokarin samun zaman lafiya a wannan kasa.

Har ilya yau , Arbor ta kuma baiyana shakar yadda aka gudanar da shari’ar wadannan mutane da kuma hukuncin kisa da aka zartas a kansu.

A bara ne dai wata kotun iraq ta sami tsohon shugaba Saddam Hussein da mataimakan sa biyu, wato tsohon babban alkali Awad Hamad al Bandar da shugaban hukumar leken asiri Barzan Ibrahim al Hassan da laifukan kisan jama’a , wanda hakan ya haifar aka gabatar da hukuncin kisa kansu.

A karshen watan Disamba r bara ne aka aiwatar da hukuncin kisa kann tsohon shugaba Saddam Hussein.