MDD tayi kira ga izraela data bawa jamian agaji daman shiga gaza | Labarai | DW | 29.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD tayi kira ga izraela data bawa jamian agaji daman shiga gaza

Mdd tayi kira ga Izreala data bawa masu kai kayan agajin gaggawa daman shiga zirin gaza domin tallafawa mutane,tare da gargadin cewa mai da zaayi amfani dashi wajen tsabtace muhalli zai kare ,nanda yan kwanaki.Dakarun Izraela dai na cigaba da kutsawa zirin gaza ,da nufin gano jamiin sojin da aka cafke tun ranar lahadi.Tun a jiya nedai dakarun Izraelan suka kaddamar da hari akan cibiyar samarda wutan lantarkin ,da kuma bututun samar da ruwa,a Gazan dake zama matsugunnin mutane million 1.4.Jakadan MDD a shirin samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya,Alvaro de Soto,yace akwai yanayi dake bukatar agajin gaggawa a yankin palasdinawan.Baya ga wutan lantarki,jakadan mdd yace,dakarun na Izraela sun kuma fasa bututun dake samarda man gudanar da tsabtar muhalli.

Mr De soto ,wanda yayi kira ga sojin sakai na palasdinu dake rike da Kofur Gilad Shalit ,dasu sake shi ,ya sanar dacewa sakatare general na mdd Kofi Annan yayi magana da prime minista Ehud Olmert na Izraela,adangane da matsalolin rayuwa da alummomin ke ciki.

Yanzu haka dai zaa dauki watanni 6-8,wajen gyaran cibiyar wutan lantarkin da Dakarun Izraelan suka tarwatsa.Naurorin da kudadensu suka kai dala million 15.