Mdd tayi barazanar dakatar da agaji a Darfur | Siyasa | DW | 28.09.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mdd tayi barazanar dakatar da agaji a Darfur

Egeland yace jamian agajin mdd na cikin hatsari na barkewan rikici

default

Babban jammiin hukumar bada agaji ta mdd Jan Egeland yayi gargadi dangane da dakatar da ayyukan agaji a lardin Darfur,dangane da sabbin rigingimu da suka fara bullo a yankin.

Mr Egeland ya bayyana cewa hali na barazana da maaikatan agajin majalisar dubu 11 ke ciki a yanzu haka,abun tsoro ne,kuma batutuwa na ire iren wadannan barazana karuwa suke a lardin darfur din,sakamakon sabbin hare hare hare da ake cigaba da kaiwa.

Ya fadawa taron manema labaru cewa ana dada samun karuwan barkewan rikici a sassa daban daban a yammacin Sudan din,sakamakon gaza aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimmawa a shekara ta 2004.

Jamiin na Mdd dake lura da dukkan harkokin tallafi na majalisar,.yace karuwan tashe tashen hankula zai iya tilastasu dakatar da agajin da suke samarwa mutane kimanin million 2.5,inda ya kara dacewa koda gobe ne,zasu iya dakatar da yayyukan agajin nasu a Darfur.

Yace zasuyi iyakar kokarinsu na cigaba da bada agaji,amma idan lamarin yaki canzawa,zai zamanto tilas su tattara su fice daga yankin,domin rayukan jamiansu na cikin hadari.

Tun day an tawaye suka kaddamar da fada a lardin darfur dake yammacin sudana a watan febrairun shekarata 2003 dai,sama da fararen hula dubu 300 suka rasa rayukansu,ayayinda samada million biyu suka rasa matsugunnensu.

Rikicin na lardin Darfur dai ya kunshi kungiyoyin yan tawaye guda biyu da suka hadar dac Sudanese Liberation Army da Justice and Equality movement,wadanda ke yakan dakarun gwamnanati,da mayakan larabawa dake kiran kansu janjaweed.Ana dai zargin Janjaweed dake zama masu marawa gwammnati baya da kai hare hare kauyukan bakaken fata dake da zama a yammacin kasar.

Mr Egeland yace wannan kamar maimaicin abunda ya faru a Yugoslavia ne a shekarun 1990s,yayinda dakarun sabiyawa suka yiwa alumman musulmi yankan rago,a yankunan dake karkashin kulawan mdd,batu daya kawo cikas cikin ayyukan agaji da majalisar ke gudanarwa.

Yace dole ne shugabannin kasashen duniya su sanya baki kamar yadda sukayi a shekarar data gabata,wajen tursasawa Sudan da kuma yan tawayen a bangare guda,na amince da hanyoyin warware wannan takaddama dake tsakaninsu.

A bara komitin sulhun mdd tayi barazanar kakabawa gwammnatin sudan takunkumi ,idan har bata karbe makaman mayakan janjaweed ba,tare da kira gay an tawayen dasu dakatar da fada.

A yanzu haka dai ana gudanar da tattaunawan sulhu tsakanin bangarorin biyu a karkashin jagorancin kungiyar gammayar Afrika Au,to sai dai babu alamun zaa cimma wani tudun dafawa.

A dangane da hakane Mr Egeland yayi kira dangane da bukatar fadada ayyukan tsaro da kungiyar ta Au ke gudanarwa ,da Karin sojoji daga sauran kasashen duniya.Yace yanzu haka akwai dakarun kiyaye zaman lafiya 5,000,amma akwai bukatar ninka wannan adadin.

A makon daya gabata nedai komitin sulhun mdd ta sanar da kara waadin dakarunta dake Darfur din da watasttni shida,wadanda yawansu ya kamata su kai dubu 10,000,ammam guda 1,708 ne kachal suke Darfur din a watan daya gabata.

 • Kwanan wata 28.09.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZL
 • Kwanan wata 28.09.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZL