1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

MDD tayi Allah wadan karuwan rikici a Darfur

default

Majalisar dunkin duniya tayi Allah wadan sabbin tashe tashen hankula da suka barke a lardin Darfur din kasar Sudan,tare da kira ga gwamnatin Khasrtum da yan tawaye dasu darajawa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma,a kokarin cimma sulhu tsakanin bangarorin biyu.

A wata sanarwar da Jakadan Romenia Mihnea Motoc,wanda ke jagorantar komitin sulhu a wannan watan ya rattaba hannu,Wakilan komitin 15 sun bayyana matukar damuwansu a dangane da rahotannin sabbin hare hare a lardin Darfur din daga dukkan bangarorin biyu,tare da gargadi agaresu dasu darajawa yarjejeniyar da aka cimma na tsagaita a 2004.

A jiya nedai aka gano gawawwakin dakarun kiyaye zaman Lafiya Nigeria biyu da suka bace tun a makon daya gabata,bayan an kai musu harin kwanton bauna.

Bugu da kari an kashe wasu dakarun Nigerian guda biyu ranar asabar data gabata,tare da wasu yan kwangila 2.A yanzu haka kuma akwa dakarun kiyaye zaman lafiyan 3 dake hali matsananci na jinya sakamakon raunuka da suka samu daga harin da aka kai musu.

Kazalika komitin sulhun takumayi Allah wadan harin da mayakan dake marawa gwamnatin khartum baya suka kaiwa matsugunnen fararen hula.

Inda tayi nuni da cewa wannan babbar matsalace dake barazana musamman wa jamian agajin MDd dake ayyukan agaji ,kuma bisa ga bincike da aka gudanar,babu alamun cewa gwamnatin kasar nada niyyan kwance damarar mayakan nata,wadanda ke cigaba da barazana wa mazauna Darfur din.

Sanarwar komitin yayi nuni dacewa suma kungiyoyin yan tawayen sun gaza shawo kann matsalolin mayakan nasu.

To sai dai duk da wannan hali da ake ciki,komitin yabada tabbacin cigaban hadin kai wa kungiyar gamayyar Afrika akokarinta na ganin cewa ,an darajawa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a baya,da kuma tattaunawar sulhu dake gudana a Abujan nigeria,akarkashin jagorancin AU din.

Tun ranar laraba nedai kakakin gwamnatin Khartum ta sanar dacewa Mdd tace rashin zaman lafiya a darfur din namai kasancewa babban hadari wa jamian agajinta.

Ta bada misalin sace jamian Au 40 da mayakan yan tawayen sukayi.

Adangane da hakane yanzu haka Mdd ta sanar dacewa dukkan jamianta da ayyukansu basu da muhimmanci ayanzu su fice daga lardin na Darfur dake fama da rikici.

Tun a watan febrairun shekarata 2003 nedai rikici ya barke a lardin Darfur tsakanin yan tawaye da mayakan janjaweed dake marawa gwamnnatin Khartum baya,fadan daya kashe akalla mutane dubu 180,baya ga wasu million 2 da dubu dari 6 da suka rasa matsugunensu.

 • Kwanan wata 14.10.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvYn
 • Kwanan wata 14.10.2005
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvYn