1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta soki lamirin kisan fararen hula a Qana.

July 31, 2006
https://p.dw.com/p/BuoT

Daukacin mambobin kwamitin sulhu na Majalisar ɗinkin duniya sun zartar da sanarwa wadda ta baiyana matuƙar jimami da kisan kan mai uwa da wabi da Israila ta yiwa fararen hula a ƙauyen Qana na ƙasar Lebanon. Sanarwar ta yi kakkausar suka ga kisan fararen hula wanɗanda basu ji ba basu gani ba. Sai dai kuma ba ta yi kiran dakatar da yaƙin cikin gaggawa ba kamar yadda sakataren Majalisar Kofi Annan ya buƙata tun da farko. Amurka ta ƙi amincewa da buƙatar tsagaita wutan cikin gaggawa. Gabanin taron kwamitin sulhun na Majalisar ɗinkin duniya, P/M Lebanon Fouad Siniora ya baiyana luguden wutar da Israilan ta yi a Qana da cewa babban laifi ne. Sanarwar kwamitin sulhun na Majalisar ɗinkin duniya ya kuma jaddada aniyar sa na cigaba da aiki ba tare da jinkiri ba domin zartar ƙudirin kawo ƙarshen rikicin baki ɗayan sa.