1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mdd ta soki lamirin kasar Amurka

Sakataren Mdd, Mr Kofi Anan yayi watsi da sukar da Amurka tayiwa mataimakin sa, bisa wasu kalamai na suka da mataimakin nasa yayi ga kasar ta Amurka.

A cewar kakakin Mdd, bayanan da Mr Mark Malloch Brown yayi, kalamaine da Kofi Anan ya amince dasu, a don haka babu wani hukunci na ladaftarwa da majalisar zata dauka a kann sa.

A dai ranar talatar data gabata ne, mataimakin na Kofi Anan, ya kalubalanci Amurka da cewa tana fakewa da Mdd wajen warware rikice rikice da suka shafi duniya, amma kuma ta gaza kare Mdd daga sukar da ake mata a cikin gida.

Wannan dai bayani, ya harzuka mahukuntan na Amurka, a inda kafafen yada labaru suka rawaito jakadan kasar a mdd, wato Mr John Bolton na cewa furucin kuskure ni mai muni, a don haka a janye a wannan furucin.