MDD ta samu izinin kai kayan agaji a Siriya | Labarai | DW | 08.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta samu izinin kai kayan agaji a Siriya

Gwamnatin Siriya ta bai wa Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Redikros izinin kai kayan agaji a wasu biranan kasar inda yaki ya rutsa da mutane tare da sakasu cikin matsalar yinwa.

Gwamnatin kasar Siriya ta bai wa Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar agaji ta Red Cross izinin kai kayan agaji a wasu biranan kasar wadanda yaki ya rutsa da mutane a cikinsu tare da sakasu cikin matsalar yinwa a 'yan watannin baya-bayan nan.

Ofishin Hukumar kula da aiyyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya wato OCHA ya ce biranan kasar ta Siriya da ke fama da wannan matsala da kuma za su ci moriyar agajin sun hada da birnin Madaya da ke a hannun 'yan tawaye da amma sojojin gwamnatin Siriya suka yi masa kofar raggo yau tsawon watanni shida, da kuma biranen Foua da Kafraya na 'yan Shi'a masu kunshe da mutane kimanin dubu 20 wadanda su kuma 'yan tawaye suka yi masu kawanya tare da saka al'ummar cikin yanayin yinwa da karancin magunguna.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniyar ta bayana gamsuwrta da wannan izini da ta samu kuma ta ce za ta soma aikin shiga da kayan agajin ba tare da bata lokaci ba.