1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mdd ta kawo karshen aikin kiyaye zaman lafiyar ta a Ivory Coast

December 15, 2005
https://p.dw.com/p/BvGN

Dakarun kiyaye zaman lafiyar kasar Pakistan 300 dake kasar Ivory Coast karkashin lemar Mdd sun bar kasar a yau izuwa gida.

Ficewar dakarun kiyaye zaman lafiyar dake mataki na karshe na a matsayin alama ce ta kawo karshen yakin basasar kasar daya halaka mutanen kasar kusan dubu 120.

Mdd dai ta kawo karshen aikin nata ne a wannan kasa , bayan data gamsu daci gaban da aka samu ta fuskar zaman lafiya.

Bugu da kari Mdd ta kara da cewa an kuma samu galabar kwancewa mayaka dubu sabain da biyar damarar yaki a kasar.

Rahotanni dai sun nunar da cewa an bar dakarun kiyayre zaman lafiya na Nigeria da yawan su ya tasamma 250 a kasar don bawa kotun tuhumar wadanda suka aikata miyagun laifuffuka tsaro da