MDD ta kada kuri´a kan wata yarjejeniyar da zata kayyade cinikin makamai | Labarai | DW | 27.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta kada kuri´a kan wata yarjejeniyar da zata kayyade cinikin makamai

Wani kwamitin MDD ya ba da damar da a ci-gaba da fasalta wani daftarin yarjejeniya ta kasa da kasa akan cinikin makamai. Burin wannan mataki shi ne a yi gyara ga dokokin da ake amfani da su yanzu wadanda suka yarda a tura makamai yankunan da ake fama da rikici a ciki duk da takunkuman sayar da makamai dake aiki. Kasashe 139 na MDD suka kada kuri´ar amincewa da wannan mataki, Amirka ce kadai ta nuna adawa yayin da China da Rasha suka yi rowar kuri´unsu. Masharhanta sun ce ko da yake za´a dauki shekaru masu yawa kafin a cimma yarjejeniyar, amma kuri´ar wani muhimmin mataki ne akan turbar da ta dace.