MDD ta girka wani matsayi na mata | Labarai | DW | 14.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta girka wani matsayi na mata

An naɗa tsofuwar shugabar' ƙasar chili Michelle Bachellet a wani sabon matsayin MDD domin kula da kyautata halin rayuwar mata a Duniya

default

Michelle Bachelet

An naɗa tsofuwar shugabar ƙasar Chile Michelle Bachelet a masayin jagorar wata sabuwar hukuma ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ake kira da suna ONU Femme domin kula da kyautata halin rayuwar mata a duniya.

Sanarwar naɗin wadda sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon ya bayyana ya jinjina wa Bachelet dangane da ƙoƙarinta na neman sulhu.

Taron majalisar ne na watan satumban bara ya amince da a girka wannan sabon masayi wanda ke daidai da muƙamin sakataran majalisar.

A cikin watan Maris da ya gabata ne Bachelet ta bar muƙamin na shugabancin ƙasar ta Chile da ta yi sunan sosai akansa.

Mawallafi : Abdurahaman Hassane

Edita       :  Ahmad Tijani Lawal