Mdd ta fiddo da rahoton almundahanar da aka tafka a iraqi | Labarai | DW | 27.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mdd ta fiddo da rahoton almundahanar da aka tafka a iraqi

Rahoton binciken almundahanar da aka tafka game da shirin da Mdd ta aiwatar a iraqi, na´a sayar da manta a sayo mata abinci, yace sama da kamfaninnika dubu biyu daga kasashe daban daban na duniya nada hannu a cikin wannan ta´asa da aka tafka.

Rahoton ya shaidar da cewa ire iren wadan nan kamfaninnika sun bayar da dan abin goro har Dalar Amurka biliyan daya da digo takwas ga tsohuwar gwamnatin Saddam Hussain.

Kwamitin daya gudanar da wannan bincike karkashin jagorancin tsohon jami´in ma´´ajiyar kota kwana ta Amurka, wato Paul Volcker ya soki lamirin Mdd da sakaci wajen rashin daukar kwakkwaran mataki na dakile aiwatar da wannan almundahana.

Wannan dai shiri na Mdd a kasar ta iraqi an kirkiro shine a shekara ta 1996, karkashin kulawar kwamitin sulhu na Mdd.