1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta fidda rahoto a kan Afghanistan

Zulaiha Abubakar
May 7, 2018

A wannan Litinin ce Majalisar Dinkin Duniya ta fidda wani rahoto wanda ke cewar yara 30 na daga cikin wadanda suka rasa ransu a Afghanistan yayin da gwamnatin kasar ta kaddamar da wani hari a yankunan 'yan ta'adda

https://p.dw.com/p/2xKPl
Afghanistan UN-Bericht 30 Kinder nach Luftschlag getötet
Hoto: picture-alliance/Xinhua News Agency/A. Kakar

Rahoton ya kara da cewar irin wadannan hare-hare da kasar ke kaiwa yankuna daban-daban ne suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 36 a ranar biyu ga wannan wata na Mayu a arewacin yankin Kunduz da ke Afghanistan, yayin da suke tsaka da gudanar da wani biki da daruruwan mutanen da suka hada da dattijai da kuma matasa suka halarta.

Koda yake kakakin rundunar tsaron kasar Mohammad Radmanish ya sanar da cewar sun samu nasarar kashe 'yan kungiyar ta'adda na Taliban talatin  a harin da suka  kai.

Tun bayan da kasar Amirka da kuma kungiyar tsaro ta NATO suka kammala aikin su na tsaro a shekara ta 2014 ne, Afghanistan din ta umarci rundunar tsaron kasar da tayi duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen Taliban da kungiyoyi masu alaka da IS a fadin kasar.