MDD ta fara rarraba abinci a Janhuriyar Niger | Labarai | DW | 25.08.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta fara rarraba abinci a Janhuriyar Niger

Mdd ta fara rabon tallafin abinci kyauta wa dubban daruruwan mutane dake fama da yunwa a janhuriyar Niger,wadda ke zama kasar dake fama da karancin abinci a yankin yammacin Afrika.Sakamakon fari da farin dango da suka lalata amfanin gona a shekaru biyu da suka gaba,alummar kasar ta Niger sun fada wani wadi na tsaka mai wuya na yunwa a shekarar data gabata.Duk dacewa kasar ta fara farfadowa daga wannan matsala,a halin yanzu ajiyayyun abinci sun fara karewa ,gabannin girbin wannan shekara.A dangane da hakane hukumar bada tallafin abinci ta mdd ta fara rarraba hatsi wa alummar janhuriyar Niger din ayau.Directan hukumar dake kasar,Sory Ouane,yace zai dauki lokaci kafin Niger ta farfado daga matsalar yunwa data fuskanta a shekarar data gabata.

 • Kwanan wata 25.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5i
 • Kwanan wata 25.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5i